Wednesday 20 January 2016

Nima Macece Episode 5 Jan 20th

If you're new read the previous episodes click here



Dawowa gidan keda wuya dama yadan siyo kajinshi yashiga gun basant ganinta yayi tana zaune yashigo my baby ya kike?. Ta dago tana murmushi don wani sonshi taji ya mamayeta. Bata tunanin kowa sai shi shine ubanta shine uwarta. Yace sauko muci kaza da hanzari tasauko yana bata abaki tanaci hartaci takoshi.
 Lokacin daya fice itama ta mike kan gado. Ruky ne tashigo kinfara sallane?. Takalleta tace meye sallah?. Ruky tayi shiru lalle malam ya iya aiki mai kyau tafdijam. Wato har ibadanta yamantar da ita. Saita tuna yace yin sallanta zai hana aikin yiwuwa shiyasa aka mantar da ita. .

Alhaji nazaune a falo shida adda wayansa tadau kara yadauka . Sai yace a a. Ahmadu yaushe zaka dawo?. Allah dawo dakai lafiya ka kammala kenan ko?. To saikazo. Yace ahmadu (dan yayanshi marigayi wanda ke zaune agidanshi tun yana yaro yafita UK. Karatun degree da masters dinshi daganan suka rikeshi yasamu aikin yi.). Juyowa yayi yacewa adda. Kinsan me?. Ahmadu nadawo tayi murmushi cikin murna tare dacewa Allah yadawo dashi lafiya. Yanzu basant tasaba suci abinci da basamude tare susha. Hatta wanka shiyake mata.(Allah zai saka mata injini Skîll) ganin yanzu ta sake shiyasa yabarta take shiga ko ina a gidan ruky kuma tazama munafukar tsakiya tana gidan alhjai tana gidan basamude.
Dawowan ahmed tamkar ni'ima ce agun su adda domin kuwa ya kwantar musu da hankali ya gwada musu cewa insha Allah yamusu alkawari zai binciko basant kasancewar fannin daya karanta kenan. Dafarko yaje yakarbo wayan basant. Dakuma takalminta da gyalenta wanda su adda suka samu. Yakuma ziyarci gidan atakaice ansanar dashi komai har zuwan ruky dasauransu yace akira mishi ita.
 Yana rubutu a office tashigo dagowa ya kalleta sama da kasa. Itakuma gaba daya tagama tsarguwa inka cire sonshi data faraji atake. Tana da kyau kam anma baiga amfanin kyan ba don yana ganin itace no.1 suspect na criminal case din. A gameda dan binciken dayayi saidai kuma yatuna its a game of intelligent criminals. Donhaka gwara shima yazo da dabara, Yakalleta yace karaso madam. Ganin kallon daya mata yasa tashigo da dan takunta tazauna tana wani yauki dashan kamahi. Ya kalleta yace ruky ko. Tace yes sir. Yayi murmushi wanda yakara bayyana mata kyansa yace you can call me Ahmed Fawu. Ta girgiza kai .
Yace so back to business please ya akayi kika ganta dasauransu? Tace nima ganinsu nayi a mota sainabisu danaga inda suka shiga sai nakoma. Tana magannanne yana kallon cikin idonta, shi yanada wani abu hakan yasashi karanta law dakuma socialogy Inya kalli tsabar idonka kana karya zaigane.(mutane ne basu ganewa anma shikanshi karya na kunyan kwayan ido duk rashin kunyan mai yinta inzaka kalleshi cikin ido tsantsa zaka gane injini kenan). Yayi murmushi yace insha Allah basant takusa dawowa. Itama murmushin tayi gaskiya kam nima nagaji naga kawalliyyata (kuji shishigiî).
Wasa wasa ahmed ya rinjaye ruky takamu dasonsa sosai sannan yana lura da duk takunta. Itakuma yanzu jitake zata iya tona asirin basamude akan ahmed. Nuna mata yakeyi yana sonta sosai. Wata rana suna zaune da ahmed din. Suna tadi saiga wayan rukyn ankira tadauka tana yamutsa fuska I'll call u later. Ahmed agogonsa yakalla time sannan yacigaba da abinda yake sunje park tare yakarbi wayanta barin yi game . Anan yaje call log dinta yaga numban dayakira exact time din daya duba agogonsa. Sannan ya haddace number.
Atake yana gamawa yace tashi mutafi tace bamu gamaba yace nagaji bacci nakeji. Dole ta tashi suka fice. Nan zamu tsaya yau sai mun hadu gobe insha Allah.


Add insidearewa official whatsapp number for update 08066680993







Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment